Kerry, Ya Bukaci Aikewa Da Dakarun MDD A Sudan Ta Kudu
Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry, ya jaddada bukatar aikewa da tawagar kiyaye zamen lafiya ta MDD wace zata kunshi dakarun Afrika a birnin Juba na Sudan ta Kudu inda gwabza kazamin fada a watan Yuli da ya gabata.
Hakazalika Mr Kerry ya yi kira ga bangarorin dake rikici a Sudan ta kudu dasu mutunta yerjejeniyar da suka cimma a shiga tsakanin MDD don kawo karshen yakin basasar daya daidaita kasar.
Mr, Kerry na bayyana hakan ne a wata hira da manema labarai bayan ganawarsa da wasu ministocin harkokin wajen kasashe biyar na gabashin Afrika a birnin Nairobi na kasar Kenya.
A ranar 12 ga watan Agusta nan ne kwamitin sulhu na MDD ya amunce da tura wata tawagar kiyaye zamen lafiya ta MDD da zata kunshi dakaru 4,000 a Juba domin kare fararen hula da dukiyoyinsu.
kafin hakan dai shugaban kasar Sudan ta kudu Salva Kiir da sabon mataimakinsa Taban Deng sunyi watsi da duk wani yunkuri na tura dakarun sulhu a kasar wanda a cewarsu ya sabawa hurimin kasar.
Rikicin daya barke a Juba a watan Yuli da ya gabata ya dai yi sanadin mutuwar mutane sama da 300 tare da cilastawa dubbai tsarewa daga gidajensu.