Faransa : Sarkozy, Zai Tsaya Takara A Zaben 2017
https://parstoday.ir/ha/news/world-i10009-faransa_sarkozy_zai_tsaya_takara_a_zaben_2017
Tsohon shugaban kasar Faransa, Nicolas Sarkozy ya bayyana anniyarsa ta tsayawa takara a zaben shugabancin kasar na shekara 2017 dake tafe.
(last modified 2018-08-22T06:58:48+00:00 )
Aug 22, 2016 11:04 UTC
  • Faransa : Sarkozy, Zai Tsaya Takara A Zaben 2017

Tsohon shugaban kasar Faransa, Nicolas Sarkozy ya bayyana anniyarsa ta tsayawa takara a zaben shugabancin kasar na shekara 2017 dake tafe.

Mr Sarkozy ya ce zai tsaya takara a zaben fidda gwamni na jam'iyyar ''les Republicains'' domin fafatawa a zaben dake tafe.

Dan shakaru 61, M. Sarkozy, wanda ya yi shugabancin kasar ta faransa a shekara 2007 zuwa 2012 ya bayyana hakan ne a shafinsa na Twitter inda ya nakalto kadan daaga cikin wani litafinsa da zai fito a wannan Laraba.

Idan dai hakan ta tabbata, Sarkozy zai fafata da shugaba mai ci Farancois Hollande a zaben mai zuwa, koda yake har yanzu M. Hollande bai bayyana aniyarsa ba a hukumance ta cewa zaiyi takata a zaben na 2017.

Saidai fa Sarkozy zai iya fuskantar kaluble iri daban daban a gabansa da suka hada da takara tsohon firaministan kasar kana magajin birnin Bordeaux Alain Juppé a zaben fidda gwani na wannan jam'iyya da kuma batun dake gaban shari'a na badakalar nan ta kudaden yakin neman zaben sa a shekara 2012.