-
Firayi Ministan Malaysia Ya Ce Tattaunawa Da Trump Abu Ne Mai Wahala
Aug 14, 2018 14:57Firayi ministan kasar Malaysia ya bayyana cewa tattaunawa da Trump abu ne mai matukar wahala domin a cikin sa’oi 24 zai iya canja ra’ayinsa.
-
Rahoton MDD Ya Ce Akwai Dubban 'Yan Ta'addan Kungiyar Da'ish A Yankin Gabas Ta Tsakiya
Aug 14, 2018 02:32Rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya sanar da cewa: Duk da nasarar da aka samu na murkushe kungiyar Da'ish a kasashen Iraki da Siriya amma har yanzu akwai dubban 'yan ta'addan kungiyar a yankin gabas ta tsakiya.
-
Shugabannin Koriya Ta Kudu Da Ta Arewa Za Su Yi Zama A pyongyang
Aug 13, 2018 08:21Shugabannin kasashen Koriya ta kudu da kuma Koriya ta arewa na shirin gudanar da wani zama a birnin pyongyang na kasar Koriya ta arewa.
-
Al'ummar Romania Suna Ci Gaba Da Zanga-Zangar Neman Rusa Gwamnatin Kasar
Aug 12, 2018 02:16Al'ummar Romania suna ci gaba da gudanar da zanga-zanga da gudanar da taron gangami a cikin dare a birnin Bucharest fadar mulkin kasar da nufin tilastawa fira ministar kasar yin murabus daga kan mukaminta.
-
An Tabbatar Da Tsohuwar Shugaban Kasar Cilly A Matsayin Shugaban Hukumar Kare Hakkin Bil'adama Ta MDD
Aug 11, 2018 02:14Babban zauren majalisar dinkin duniya ta amince da Michelle Bachelet tsohuwar shugaban kasar Chilly a matsayin sabon shugaban hukumar kare hakkin bil'adama ta majalisar dinkin duniya.
-
Hukumar Kula Da Makamashi ta Duniya Ta Yi Gargadi Kan Sanya Takunkumin Man Fetir A Kan Iran
Aug 10, 2018 14:26Cikin wani sabon rahoto da ta fitar Hukumar kula da Makamashi ta Duniya, IEA,ta ce takukumin da Amurka ta kakabawa Iran na sayar da man fetir, idan ya fara aiki zai dagula kasuwar man fetir a Duniya
-
Fira Ministan Rasha Ya Gargadi Kasar Amurka Kan Sake Kakaba Takunkumi Kan Kasarsa
Aug 10, 2018 07:55Fira ministan Rasha ya gargadi kasar Amurka kan sake kakaba takunkumi kan kasarsa da cewa: Kakaba takunkumin yana matsayin shelanta yakin kasuwanci ne a tsakanin kasashen biyu.
-
Rasha ta bayyana sabon takunkumin Amurka akanta da cewa ya sabawa dokokin kasa da kasa
Aug 10, 2018 02:06Kakafin fadar mulkin Libya ta Krimline Dmitry Pesco ne ya bayyana sabbin takunkuman na Amurka da wadanda suke cin karo da dokokin kasa da kasa
-
Kasa Ta Sake Girgiza A Indonusiya
Aug 09, 2018 10:54Kwanaki hudu bayan mummunar girgiza kasa data auka wa tsibirin Lombok, na Indonusiya, wata girgiza kasa mai karfin maki 6,2 ta sake auka wa yankin a yau Alhamis.
-
Rasha Ta Sha Alwashin Maida Martani Kan Sabbin Takunkuman Amurka
Aug 09, 2018 09:26Kasar Rasha ta ce tana nan tana nazarin martanin da zata mayar kan sabbin takunkuman da Amurka ta sanar, wadanda ta ce suna da alaka da harin sinadari mai guba da aka wa tsohon jami'in leken asirin Rasha nan da 'yarsa a Birtaniya cewa da Sergueï Skripal.