Rasha Ta Sha Alwashin Maida Martani Kan Sabbin Takunkuman Amurka
Kasar Rasha ta ce tana nan tana nazarin martanin da zata mayar kan sabbin takunkuman da Amurka ta sanar, wadanda ta ce suna da alaka da harin sinadari mai guba da aka wa tsohon jami'in leken asirin Rasha nan da 'yarsa a Birtaniya cewa da Sergueï Skripal.
Da take bayyana hakan a yau Alhamis, kakakin ma'aikatar diflomatsiyan Rasha , Maria Zakharova, ta ce mahukuntan Moscow na nan na nazarin irin martanin da zasu mayar kan sabbin takunkuman na Amurka.
Rasha ta ce sabbin takunkuman na Washington basu da tushe, kuma Rasha ba zata taba amunce wa da irin hakan ba.
Jami'ar ta ce an zargi mahukuntan na Rasha da yin amfani da sinadirai masu guda na soji, alhali har yanzu Biritaniya bata ma bada shaida ko guda ba akan hannun Rasha a yunkurin hallaka tsohon jami'in Skripal da 'yarsa ba.