Pars Today
Ma'aikatar tsaron kasar ta Aljeriya ce ta sanar da kame mutanen su 6 a garin Tiyaret da ke da nisan kilo mita 300 daga babban birnin kasar.
Jami'an tsaron kasar ta Aljeriya sun kame 'yan hamayyar ne da suke yin kira ga shugaba Abdulaziz Buteflika da ya yi murabus.
Babban kwamandan sojojin kasar Aljeriya ya bada labarin cewar ya tura sojojinsa tare da isassun kayakin aiki zuwa kan iyakokin kasar da kasar Libya sanadiyar tashe-tashen hankula na baya-bayan nan a kasar ta Libya.
Gwamnatin kasar Aljeriya ta kara tsanata tsaro a kan iyakokinta da kasashen da ke makwaftaka da ita, da nufin ganin ta dakushe yunkurin 'yan ta'adda na kutsa kai a cikin kasarta.
Ofishin shugaban kasar Aljeriya ya sanar da sauke fira ministan kasar Abdulmajid Tabun watanni uku bayan nada shi.
Ma'aikatar tsaron Aljeriya ta sanar da rusa wasu maboyar 'yan ta'adda guda biyu a yankin yammacin birnin Aljes fadar mulkin kasar.
Ministan harkokin wajen kasar Aljeriya Abdul-Qadir Messahel ya kai ziyarar aiki zuwa birnin Bagadaza fadar mulkin kasar Iraki, inda ya gana da jami'an kasar da nufin karfafa alakar da ke tsakanin kasashen biyu.
Majiyoyin tsaron kasar Nijar sun bayyana cewar an tsinci gawarwakin wasu ‘yan sandan kasar su uku a dajin da ke kan iyakan kasar da kasar Aljeriya.
Ministocin harkokin wajen kasashen Aljeriya da Masar sun jaddada bukatar karfafa taimakekkeniya a tsakaninsu a fagen yaki da ayyukan ta'addanci tare da jaddada wajabcin samun hadin kan duniya da nufin warware rikicin kasar Libiya.
Ma'aikatar tsaron kasar Algeria ta bayyana cewa sojojin kasar sun halaka yan ta'adda 6 a wata unguwa a kudancin birnin Algies babban birnin kasar a yau litinin.