Aljeriya Ta Tura Sojojinta Zuwa Kan Iyakokin Kasar Da Libiya
(last modified Mon, 04 Sep 2017 19:10:46 GMT )
Sep 04, 2017 19:10 UTC
  • Aljeriya Ta Tura Sojojinta Zuwa Kan Iyakokin Kasar Da Libiya

Babban kwamandan sojojin kasar Aljeriya ya bada labarin cewar ya tura sojojinsa tare da isassun kayakin aiki zuwa kan iyakokin kasar da kasar Libya sanadiyar tashe-tashen hankula na baya-bayan nan a kasar ta Libya.

Jaridar Al-bilad ta kasar Algeria a shafinta na yanar gizo ta nakalto majiyar rundunar sojojin kasa ta kasar tana fadar haka a yau litinin, sannan ta kara da cewa ta aike da sojoji 3000 zuwa kan iyakokin kasashen biyu wanda yake da tsawon kilomita 980 don tabbatar da ba wani dan ta'adda da ya shigo kasar daga kasar Libya sanadiyyar tashe-tshen hankula a kasar ta Libya. 

Banda haka labarin ya kara da cewa rundunar zata kara wasu sojojin masu sintiri da kuma isassun kayan aiki don kula da kan iyakokin kasashen biyu masu fadi. Sannan za'a kara yawan wuraren binciken masu shigowa kasar da kuma a cikin garuruwan da suke kan iyakokin kasashen biyu don tabbatar da tsaro a yankin.