An Sauke Fira Ministan Aljeriya Watanni Uku Da Nada Shi
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i23218-an_sauke_fira_ministan_aljeriya_watanni_uku_da_nada_shi
Ofishin shugaban kasar Aljeriya ya sanar da sauke fira ministan kasar Abdulmajid Tabun watanni uku bayan nada shi.
(last modified 2018-08-22T07:00:32+00:00 )
Aug 15, 2017 13:14 UTC
  • An Sauke Fira Ministan Aljeriya Watanni Uku Da Nada Shi

Ofishin shugaban kasar Aljeriya ya sanar da sauke fira ministan kasar Abdulmajid Tabun watanni uku bayan nada shi.

Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, kamfanin dillancin labaran Aljeriya ya sanar da cewa, shugaba Butaflika ya sauke Abdulmajid Tabun daga kan mukaminsa na fira minista, ya kuma nada Ahmad Ouyahiya a matsayinsa.

Tabun dan shekaru 71 zai bar mukaminsa na fira ministan kasar ta Algeriya ga Ahmad Ouyahiya, wanda yake a matsayin ministan harkokin cikin a gwamnatinsa.

Babu wasu ciakkun bayanai dangane da dalilin sauke Almajid daga kan matsayinsa, amma dai wasu majiyoyi a cikin gwamnatin Aljeriya sun kwarmata cewa, ana yawan samun sabanin ra'yi ne tsakaninsa da shugaba Butaflika.