Pars Today
Kungiyar kare hakin bil-adama ta sanar da hallakar mutane 15 yayin wani rikici da ya kuno kai a lokacin yakin zaben raba gardama kan tazartan shugaba Nkurunziza.
Kamfanin dillancin Anatoly na kasar Turkiya ya ambato majalisar harkokin wajen kasar Canada tana sanar da hana yan asalin kasar Burundi mazaunanta, kada kuri'ar raba gardama akan zaben 2018.
Rahotanni daga kasar Burundi sun bayyana cewar alal akalla mutane 26 sun mutu kana wasu da dama kuma sun sami raunuka sakamakon hari da wasu mahara suka kai lardin Cibitoke da ke arewa masu yammacin kasar.
A Wani hari da wani gungu masu dauke da makamai suka kai wasu kauyuka na arewa masu yammacin kasar Burindi, kimanin mutane 26 suka rasa rayukansu yayin da wasu 10 na daban suka jikkata
'Yan Sandan Burundi sun sanar da cewa bam din ya tashi ne a gundumar Kayanza da ke arewacin kasar.
Shugaban kasar Burundi Pierre Nkurunziza ya gudanar da wani garambawul a cikin majlaisar ministocin kasar.
Shugaban kwamitin kare hakkin bil adama na kasar Burundi Jean Baptiste Baribonezeka ya mayar da martani ga kwamitin kare hakkin bil adama na MDD, dangane da zargin kisan kiyashi a kasar ta Burundi.
Yan sanda a kasar Burundi sun bada labarin shigowar dubban yan kasar Demokradiyyar Kongo cikin kasar sanadiyar yaki tsakanin yan tawaye da sojojin a kasar.
Kasashen Tanzaniya Da Burundi sun soki kotun hukunta laifuka ta kasa kasa game da kudurin da ta dauka na gudanar da bincike kan take hakin bil-adama a kasar Burundi.
Gwamnatin ta Burundi ta yi watsi da bude binciken da kotun duniyar za ta yi akan ko an aikata laifuka akan bil'adama a kasar.