Uganda Da Tanzaniya Sun Soki Kotun ICC Kan Kasar Burundi
Kasashen Tanzaniya Da Burundi sun soki kotun hukunta laifuka ta kasa kasa game da kudurin da ta dauka na gudanar da bincike kan take hakin bil-adama a kasar Burundi.
A yayin ganawarsu da ta gudanar a yammacin kasar Uganda jiya Assabar, shugabanin kasashen Tanzaniya da Uganda John Magufuli da Yoweri Museveni sun bayyana ce matakin da kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa ta dauka zai kawo cikas na kokarin kungiyar bunkasa tattakin arzikin kasashen yammacin Afirka take yi na magance rikicin kasar Burundi.
Kungiyar ta kafa wani kwamiti na magance rikicin kasar Burundi bisa jagorancin shugaban kasar Tanzaniya mai ci da kuma tsohon shugaban kasar Benjamin Mkapa.
A bangare guda an nada Shugaban kasar Tanzaniya dake rike da jagorancin kungiyar bunkasa tattalin arzikin Afirka IGAD a matsayin mai shiga tsakani a tattaunawar a bangarorin siyasar kasar Burundin ke yi.
A ranar Alkhamis din da ta gabata ce Kotun hukunta manyan laifuka ta Duniya ICC ta bayar da umarnin gudanar da bincike a game yiyuwar take hakin bil-adama daga shekarar 2015 zuwa 2017 a kasar Burundi.