Wani Dan Sanda Cikin Maye Ya Kashe Mutum 4 A Burundi
A kasar Burundi kuma, wani jami'in dan sanda ne a cikin maye ya bude wuta kan jama'a inda ya kashe abokin aikinsa da kuma wasu fararen hula uku.
Dan sanda ya yi amfani da bindiga kirar AK-47 a lokacin da ya budewa wadannan mutane wuta, a wani wurin shakatawa a garin Gatumba da ke gabashin Bujumbura babban birnin kasar.
Da take tabbatar da hakan, ma'aikatar tsaron al'umma ta kasar Burundi ta ce za'a gurfanar da dan sandan, saboda ganganci a cikin aikinsa wanda ya kai ga hallaka mutane.
Bayanai sun nuna cewa lamarin ya faru ne bayan wani rikici, inda dan sanda ya dauko bindigarsa kirar Klashinkuf, ya kuma bude wuta kan jama'ar dake wurin, inda ya kashe mutum hudu da kuma raunata wasu hudu na daban.
Lamarin dai na zuwa ne bayan wani umarni da sfeta-janar na 'yan sanda kasar ta Burundi ya bayar na haramta wa jami'an 'yan sanda kasar yawo da bindiga ko gurneti ko kuma sanya kakin jami'an tsaro a wasu wuraren shakatawa.
A Burundi dai an jima ana korafi akan yadda jami'an 'yan sanda ke yawo dauke da manyan makamai, inda harma ake zarginsu da aikata ba daidai ba, wanda ya hada da fashi da makami.