Burundi Ta Maida Martani Ga Kotun Manyan Laifuka Ta Duniya
(last modified Sat, 11 Nov 2017 06:46:11 GMT )
Nov 11, 2017 06:46 UTC
  • Burundi Ta Maida Martani Ga Kotun Manyan Laifuka Ta Duniya

Gwamnatin ta Burundi ta yi watsi da bude binciken da kotun duniyar za ta yi akan ko an aikata laifuka akan bil'adama a kasar.

Kamfanin dillancin labarun Faransa ta ambato babban mai shigar da kara na kasar Burundi Aimée Laurentine Kanyana yana cewa; Gwamnatin kasar ta dau kudurin yin watsi da shirin kotun kasa da kasa ta manyan laifuka na bude bincike akan rikicin da ya faru a kasar shekaru biyu da suka gabata.

Kanyana ya kara cewa; Kasar Burundi ta fice daga cikin kotun duniyar ta manyan laifuka tun a ranar 27 ga watan Oktoba, kuma gabanin ficewarta, ba ta sami labari akan shirin binciken ba, bayan ficewarta kuma ba ta da wata alaka da ita.

A ranar alhamis din da ta gabata ne dai kotun manyan laifukan ta kasa da kasa ta bada umarnin a bude bincike ko an aikata laifi akan bil'adama a kasar ta Burundi daga 2015 zuwa 2017.

A wannan tsakanin kasar ta Budundi ta yi fama da cikicin siyasa sanadiyyar tazarcen shugaba Peer Nkurinziza.