Apr 30, 2017 16:46
Gwamnatin Turkiyya ta sanar da korar wasu jami'ai da ma'aikatan gwamnati kimanin 4,000 a ci gaba da diran mikiyan da gwamnatin take yi kan wadanda ta zarga da hannun cikin juyin mulkin da aka so yi wa shugaban kasar Rajab Tayyib Erdogan da bai yi nasara ba a bara.