Shugabannin Iran Da Turkiya Sun Gana A Birnin Islam-abad Na Pakistan
A gefen zaman shugabannin kasashe mambobi a kungiyar bunkasa harkokin tattalin arziki ta ECO a birnin Islam-abad na kasar Pakistan, shugabannin kasashen Iran da Turkiya sun gudanar da wata tattaunawa.
A yayin ganawar shugaba Hassan Rauhani na Iran ya bayyana cewa, kyautatar alaka a tsakanin Iran da Turkiya zai taimaka wajen warware matsaloli da dama da ake fama da su a yankin.
Rauhani ya kara da cewa, Iran da Turkiya su ne kasashe biyu mafi girma a yankin wadanda za su iya taka gagarumar rawa wajen tababtar tsaro da dawo da zaman lafiya a gabas ta tsakiya.
Haka nan kuam Rauhani ya kara da cewa, a kowane lokaci Iran tana mai imanin cewa matsaloli na siyasa da ake fama da su a yankin gabas ta tsakiya za a iya warware su ne kawai ta hanyoyi na fahimtar juna da diflomasiyya, ba ta hanyar yin amfani da karfi a kan wani bangare da ake da sabanin siyasa da shi ba.
Shi ma a nasa bangaren shugaban Turkiya Rajab tayyib Erdogan ya ce akwai kyakkyawar alaka ta fuskanci kasuwanci da tattalin arziki tsakanin Iran da Turkiya, kuma bangarorin biyu za su yi aiki a bangaren yaki da ta'addanci.