-
Fira Ministan Iraki Ya Yi Gargadin Daukan Matakin Soji Kan Yankin Kurdawan Kasar
Sep 17, 2017 06:32Fira ministan Iraki ya gargadi mahukuntan yankin Kurdawan kasar da cewa matukar aniyarsu ta gudanar da zaben jin ra'ayin jama'a kan neman ballewa daga kasar Iraki ta haifar da bullar rikici a kasar, to babu makawa gwamnatin Iraki zata dauki matakin soji domin dakatar da lamarin.
-
Iraki : An Tsige Gwamnan Kirkuk
Sep 14, 2017 16:32Majalisar tarayya a Iraki ta amunce da gagarimin rinjaye da tsige gwamnan yankin Kirkuk, Najm Eddine Karim saboda nuna goyan bayansa ga kiran zaben raba gardama na kafa kasar Kurdawa.
-
Iraki : Hare-hare IS Sun Yi Ajalin Mutum A Kalla 52
Sep 14, 2017 16:03Kungiyar 'yan ta'adda ta IS ko kuma Da'esh ta dauki alhakin kai jerin hare-haren da suka yi sanadin mutuwar mutane a kalla 52 a kusancin Bagadaza babban birnin kasar.
-
Yan Ta'adda Daga Kasashen Turai Kimani 2500 Suka Yi Yaki Tare Da'esh A Kasashen Siriya Da Iraqi
Sep 12, 2017 18:57Jami'i mai kula da yaki da ayyukan ta'addanci a kungiyar tarayyar Turai ya bayyana cewa yan ta'adda daga kasashen turai kimani 2500 ne suka je kasashen Siriya da Iraki don yaki a bangaren kungiyoyin yan ta'adda a kasashen
-
Majalisar Dokokin Kasar Iraqi Ta Ki Amincewa Da Bellewar Yankin Kurdawan Kasar Da Babban Rinjaye
Sep 12, 2017 18:54A yau talata ce majalisar dokokin kasar Iraqi ta kada kuri'ar rashin amincewa da zaben raba gardama wanda gwamnatin lardin Kurdawa na kasar suka kuduri anniyar gudanarwa a karshen wannan watan.
-
Yan Ta'addan Kungiyar Da'ish Sun Kashe Mutane 12 A Garin Karkuk Na Kasar Iraki
Sep 08, 2017 06:37Yan ta'addan kungiyar Da'ish sun aiwatar da kisan gilla kan wasu Irakawa fararen hula 12 a yankin Alhuwaijah da shiyar kudu maso yammacin garin Karkuk na kasar Iraki.
-
Kungiyar Kasashen Larabawa Ta Taya Al'ummar Iraki Murnar Samun Nasara Kan Kungiyar Da'ish
Sep 02, 2017 19:13Babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen Larabawa ya mika sakon murnarsa ga gwamnatin Iraki da al'ummar kasar kan nasarar da suka samu na yantar da garin Tala'afar da ke lardin Nainawa daga mamayar 'yan ta'addan kungiyar Da'ish.
-
Firayi Ministan Iraki Ya Sanar Da Kwato Garin Tel Afar Daga Hannun 'Yan Ta'addan Da'esh
Aug 31, 2017 17:55Firayi ministan kasar Iraki Haider al-Abadi ya sanar da cewa dakarun kasar sun sami nasarar kwato dukkanin garin Tel Afar da kuma dukkanin lardin Ninawah na kasar daga hannun 'yan ta'addan kungiyar Da'esh da ke rike da lardin na tsawon lokaci.
-
Iraki: An Kashe 'Yan Da'esh 130 Da Suke Gudu Daga Talla'afar
Aug 30, 2017 06:56Sojojin Peshmarga na Kurdawa ne suka sanar da kashe 'yan Da'esh da suka gudo daga garin Talla'afar.
-
Dakarun Kurdawar Kasar Iraki Sun Kashe 'Yan Ta'addan Kungiyar Da'ish Fiye Da 130
Aug 29, 2017 18:56Dakarun yankin Kurdawa mai cin kwarya-kwaryar gashin kai a kasar Iraki sun kashe mayakan kungiyar ta'addanci ta Da'ish fiye da 130 a kokarin da 'yan ta'addan suke yi na tsallakawa cikin kasar Siriya bayan da aka fatattake su daga garin Tala'afar na Iraki.