Iraki : Hare-hare IS Sun Yi Ajalin Mutum A Kalla 52
Kungiyar 'yan ta'adda ta IS ko kuma Da'esh ta dauki alhakin kai jerin hare-haren da suka yi sanadin mutuwar mutane a kalla 52 a kusancin Bagadaza babban birnin kasar.
Ko baya ga wadanda suka rasa rayukansu da akwai wasu sama da 90 da suka raunana, a yayin da wasu bayanai ke cewa akwai yiyuwar adadin wadanda suka mutu ya karu saboda munanen raunukan da suka samu.
Hare-haren wadanda aka kai da bindiga da kuma mota an dai kai su ne a wani gidan cin abunci dake birnin Nassiriya a nisan kilomita 300 daga birnin Bagadaza a yankin Zi Qar wanda yanki ne da ba'a cika samun tashe tashe hankula ba.
Harin na biyu kuwa wanda aka kai da mota an kai shi ne a wani shingen bincike na jami'an tsaro dake kan wata babbar hanya inda masu yawan bude ido da masu ziyara ke bi zuwa wurare masu tsarki na 'yan shi'a a biranen Najaf da Karbala.
A cikin wata gajeriya sanarwa data wallafa a shafinta na farfaganda Amaq, kungiyar 'yan ta'adda ta Da'esh ta ce i'yan kunar bakin wakenta da dama ne suka kai harin.