Pars Today
A yau talata ne 'yan ta'addar kungiyar Da'esh da ke cikin kasar Syria su ka yi kokarin kutsawa cikin Iraki, sai dai dakarun sa-kai na Hashdu-Sha'aby sun yi nasarar dakile harin
Rahotanni daga Iraki, na cewa mutane a kalla 16 ne suka rasa rayukansu, kana wasu kimanin talatin suka jikkata, biyo bayan fashewar wani rumbun makamai a Bagadaza babban birnin kasar.
Ofishin Majalisar Dinkin Duniya da ke kasar Iraki "UNAMI" ya sanar da cewa: Duk da kawo karshen mamayar kungiyar ta'addanci ta Da'ish a kasar amma matsalar tashe -tashen hankula a Iraki a cikin wata guda kacal sun lashe rayukan mutane akalla 95.
Majalisar wakilai a kasar Amurka ta sanya wasu kungiyoyi ukku wadanda suke cikin kungiyoyin da suka yaki kungiyar yan ta'adda ta Daesh a kasar cikin jerin kungiyoyin yan ta'adda a wajenta.
Ma'aikatar cikin gidan Iraki ta sanar da cewa babu wata matsala ta tsaro da aka samu a yayin da al'ummar kasar ke ci gaba da zaben wakilansu na Majalisar dokoki.
Wata kotu a Iraki ta yanke hukuncin daurin rai da rai a kan wasu mata 19 yan kasar Rasha, bayan samun su da laifin shiga kungiyar 'yan ta'adda ta (IS) a Iraki.
Kakakin ma'ikatar tsaron kasar Iraki ya tabbatar da tuntubar hukumomin kasashen Siriya,Iran da Rasha kafin suka kaddamar da harin sama kan maboyar 'yan ta'addar ISIS a kan iyakar kasar da Siriya.
Gwamanatin kasar Iraki ta sanar da cewa sojin saman sun kaddamar da wasu munanan hare-hare kan sansanonin 'yan kungiyar ta'addancin nan ta Daesh da suke cikin kasar Siriya a kokarin da kasahen biyu suke yi na ganin bayan wannan kungiyar ta ta'addanci a kasashen biyu.
Babban Mai ba da Shawara akan harkokin Tsaro na Iraki ne ya shaida wa tashar talabijin din almayadeen cewa; Wajibi ne a kayyada adadin masu bada shawarar a harkokin soja na Amurka da za su kasance a cikin Iraki
Ma'aikatar shari'a kasar Iraki ta bayyana cewar an zartar da hukuncin kisa kan 'yan ta'adda guda 11 a wadanda wata kotu a kasar ta tabbatar da laifin aiwatar da ayyukan ta'addanci daban daban a kasar.