Iraki Ta Ki Amincewa Da Girke Sojojin Amurka A cikin Kasarta
Babban Mai ba da Shawara akan harkokin Tsaro na Iraki ne ya shaida wa tashar talabijin din almayadeen cewa; Wajibi ne a kayyada adadin masu bada shawarar a harkokin soja na Amurka da za su kasance a cikin Iraki
Falih Fayyadh ya ci gaba da cewa; Kasarsa tana aiki kafada da kafada da kasar Syria a fagen fada da ta'addanci, wanda hakan yake nuni da yadda kasashen biyu su ka yi tarayya akan batutuwan da su ke gabansu.
Falih ya kuma bayyana matsayar kasarsa na kin amincewa da aika sojoji zuwa kasar Syria kamar yadda Amurka ta bukata sannan ya kara da cewa: Baya ga barna da ta'adin da ke tattare da daukar mataki irin wannan, yana kuma kunshe da cin kudade masu yawa.
Dangane da zaben da ke tafe a Iraki ya yi fatan ganin zai kawo karshen tsoma bakin da kasashen waje suke yi a harkokin cikin gidan kasar.