Mutane 16 Sun Mutu A Fashewar Rumbun Makamai A Iraki
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i31498-mutane_16_sun_mutu_a_fashewar_rumbun_makamai_a_iraki
Rahotanni daga Iraki, na cewa mutane a kalla 16 ne suka rasa rayukansu, kana wasu kimanin talatin suka jikkata, biyo bayan fashewar wani rumbun makamai a Bagadaza babban birnin kasar.
(last modified 2018-08-22T07:01:56+00:00 )
Jun 07, 2018 01:16 UTC
  • Mutane 16 Sun Mutu A Fashewar Rumbun Makamai A Iraki

Rahotanni daga Iraki, na cewa mutane a kalla 16 ne suka rasa rayukansu, kana wasu kimanin talatin suka jikkata, biyo bayan fashewar wani rumbun makamai a Bagadaza babban birnin kasar.

Lamarin dai ya auku ne a cikin daren jiya Laraba, a unguwar Sadr City, kusa da wani masallaci, kuma tuni jami'an tsaro suka kaddamar da bincike don gano musababin aukuwar lamarin.

Mafi yawan wadanda lamarin ya rusa dasu yara da mata ne, a cewar majiyoyin asibiti dana tsaro.

Wani babban jami'in 'yan sanda ya shaida wa kamfanin dilancin labaren AFP cewa, rashewar ta auku ne a gidan gungun wasu masu dauke da makamai.

Bayanai sun ce an kuma samu barna mai yawa a unguwar, inda gidaje da dama da kuma motoci suka lalace.

Sadr City, nan ne dai unguwar da malamin 'yan shi'a nan Irakin, da ya lashe zaben 'yan majalisar dokokin baya bayan nan ke da nazauni.