-
Kasar Uganda Ta Yi Kiran Da A Gaggauta Aiwatar Da Yarjejeniyoyin Da Ke Tsakaninta Da Iran
Jan 13, 2018 17:07Ma'aikatar harkokin wajen kasar Uganda ta jaddada wajibcin gaggauta aiwatar da yarjejeniyoyin da aka cimma tsakanin kasar da Jamhuriyar Musulunci ta Iran a fagage daban-daban.
-
Iran Ba Za Ta Girmama Wani Abu Sama Da Abin Da Aka Cimma A Yarjejeniyar Nukiliya Ba
Jan 13, 2018 17:06Ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran ta bayyana cewar Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba za ta girmama duk wani abu sama da abin da aka cimma a yarjejeniyar nukiliyar da ta cimma da manyan kasashen duniya a shekara ta 2015 ba.
-
Shugaban Faransa Ya Zanta ta Wayar Tarho Da Takwaransa Na Amurka Kan Iran
Jan 12, 2018 06:35Emmanuel Macron shugaban kasra Faransa ya tattauna ta wayan tarho da takwaransa na kasar Amurka Donald Trump inda ya bayyana masa muhimmancin ci gaba da mutunta yerjejeniyar nukliya tsakanin Iran da Kasashe 5+1.
-
Yarjejeniyar Nukiliya: Martanin Iran Da Tarayyar Turai Ga Shugaban Kasar Amurka
Jan 11, 2018 11:09A yau alhamis ne ake ganawa a tsakanin ministan harkokin Wajen Iran da takwarorinsa na turai, domin jaddada riko da yarjejeniyar Nukiliya
-
Zarif: Iran Za Ta Ci Gaba Da Riko Da Yajejeniyar Nukiliya Ne Idan Amurka Ta Girmama Ta
Jan 11, 2018 05:48Ministan harkokin wajen kasar Iran Dakta Muhammad Jawad Zarif ya bayyana cewar Jamhuriyar Musulunci ta Iran za ta ci gaba da girmama yarjejeniyar nukiliyan da aka cimma da ita ne matukar dai Amurka ta ci gaba da girmama yarjejeniyar ba tare da yi mata karan tsaye ba.
-
Ministan Tsaron Iran Ya Ce Amurka Za Ta Fuskanci Mai Da Martani Daga Iran
Jan 10, 2018 11:23Ministan tsaron kasar Iran Birgediya Janar Amir Hatami ya bayyana cewar Amurka za ta fuskanci kakkausar mai da martani saboda hasarorin da ta janyo wa Iran sakamakon fitinar baya-bayan nan kamar yadda ta fuskanta a dukkanin fitinar da ta haifar a Iran.
-
Jagora: Al'ummar Iran Sun Kunyata Amurka, Birtaniyya Da 'Yan Amshin Shatansu
Jan 09, 2018 11:22Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewar cewa al'ummar Iran sun kunyata Amurka, Birtaniyya da sauran 'yan amshin shatansu yayin da suka fito don nuna goyon bayansu ga tsarin Musulunci da kuma yin Allah wadai da masu tada fitina.
-
Zarif: Saudiyya, Amurka Da Isra'ila Su Ne Masu Kunna Wutar Rikici A G/Tsakiya
Jan 08, 2018 11:21Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa Saudiyya, Amurka Da haramtacciyar kasar Isra'ila su ne suke kunna wutar fitina da rikice-rikice a yankin Gabas ta tsakiya da hanyar siyasarsu ta mulkin mallaka da suke gudanarwa.
-
'Yan Sandan Iran Sun Ce An Kama Manya Daga Cikin Wadanda Suka Kitsa Rikicin Da Ya Faru A Kasar
Jan 07, 2018 11:11Rundunar 'yan sandan kasar Iran ta bayyana cewar jami'anta sun sami nasarar ganowa da kuma kame dukkanin wadanda suka tsara da kuma aiwatar da rikice-rikicen da ya faru na baya-bayan nan a wasu garuruwa na kasar.
-
An Kara Gudanar Da Zanga-Zangar Goyon Bayan Gwamnati A Nan Iran
Jan 06, 2018 19:04Dubban dubatan mutane sun fito kan tituna a garuruwa da dama, kwanaki hudu a jere suna nuna goyon bayansu ga tsarin musulunci da kuma shugabanci a kasar Iran.