An Kara Gudanar Da Zanga-Zangar Goyon Bayan Gwamnati A Nan Iran
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i27067-an_kara_gudanar_da_zanga_zangar_goyon_bayan_gwamnati_a_nan_iran
Dubban dubatan mutane sun fito kan tituna a garuruwa da dama, kwanaki hudu a jere suna nuna goyon bayansu ga tsarin musulunci da kuma shugabanci a kasar Iran.
(last modified 2018-08-22T11:31:15+00:00 )
Jan 06, 2018 19:04 UTC
  • An Kara Gudanar Da Zanga-Zangar Goyon Bayan Gwamnati A Nan Iran

Dubban dubatan mutane sun fito kan tituna a garuruwa da dama, kwanaki hudu a jere suna nuna goyon bayansu ga tsarin musulunci da kuma shugabanci a kasar Iran.

Tashar Talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa na gudanar da zanga-zangar goyon bayan gwamnati a nan Tehran da wasu garuruwa wadanda suka hada da, Sari, Amol da kuma Semnan daga arewacin kasar. Sannan garin Ilam daga yammacin kasar, sai kuma garin Kerman daga kudancin kasar.

Kamar sauran kwanakin da suka gabata mutanen sun yi Allah wadai da tada fita, da kuma lalata dukiyoyi ko kuma kashe mutanen ba basu jiba basu gani ba. 

Ana gudanar da wadannan zanga-zanga ne don yin  Allah wadai da wasu bata gari wadanda suka shigo cikin masu zanga-zangar neman saukin rayuwa suka karkatata zuwa tashe-tashen hankula wadanda suka kai ga mutuwar mutane da dama. 

Mafi yawan wadanda suka jagorancin fitinar dai suna samun tallafi ne daga kasashen waje musamman gwamnatin Amurka, Haramtacciyar kasar Isaraila da kuma Saudia.