-
A Yau Laraba Ne Za A Gudanar Da Taron Tattaunawa Karo Na 4 Tsakanin Faransa Da Iran
Dec 20, 2017 02:50A yau Laraba ne mataimkain ministan harkokin wajen kasar Iran a bangaren sharia Abbas Araqchi zai fara tattaunawa karo na 4 tsakanin Faransa da Iran a birnin Paris.
-
Iran Ta Yi Allah Wadai Da Hawa Kujerar Nakin Da Amurka Ta Yi Kan Qudus
Dec 19, 2017 02:05Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi kakkausar suka da kuma Allah wadai da hawa kujerar nakin da Amurka ta yi dangane da kudurin Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniay da ya bukaci Amurkan da ta janye sanarwar da ta yi na amincewa da birnin Kudus a matsayin babban birnin haramtacciyar kasar Isra'ila.
-
Babban Sakataren MDD Ya Maida Martani Ga Kafafen Yada Labaran Amurka Dangane Da Shirin Nukliyar Kasar Iran
Dec 18, 2017 15:42Babban saktaren Majalisar dinkin duniya Antonio Guteres ya musanta labaran da kafafen yada labaran Amurka suka yada na cewa Iran ta sabawa kudurin MDD na 2231 kan shirin Nukliyar kasar.
-
Zarif:Iran Za Ta Kai Karar Amurka A Gaban MDD
Dec 17, 2017 03:07Ministan harakokin wajen Iran ya tabbatar da cewa Jamhuriyar musulinci ta Iran za ta shigar da karar Amurka a gaban Majalisar dinkin Duniya kan da'awar da wakiliyar Amurka a MDD ta yi na cewa Iran din na bawa kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen makamai.
-
Sheikh Siddiqi: Makiya Sun Kirkiro Daesh (ISIS) Ne Don Kare H.K.Isra'ila
Dec 15, 2017 12:09Wanda ya jagoranci sallar Juma'ar birnin Tehran, Hujjatul Islam wal Muslimin Kazim Siddiqi ya bayyana cewar makiya sun kirkiro kungiyar Da'esh (ISIS) ne da nufin tabbatar da tsaron haramtacciyar kasar Isra'ila, to sai dai sun gagara cimma wannan bakar aniya ta su.
-
MDD Ta Yi Watsi Da Kalaman Jakadiyar Amurka A Majalisar Kan Iran
Dec 15, 2017 12:08Mataimakin kakakin babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Farhan Haq, ya bayyana cewar babu wata hujja da take tabbatar da cewa makamai masu linzamin da dakarun kasar Yemen suka harba cikin Saudiyya kirar Iran ne kuma Iran ce ta ba su.
-
Iran Ta Yi Watsi Da Zargin Mikawa 'Yan Houtsi Makami Mai Linzami
Dec 15, 2017 00:59Jamhuriya Musulinci ta Iran, ta yi watsi kwata kwata da zarge-zarge marar tushe da jakadiyar Amurka a MDD, Nikki Haley, ta yi, na cewa makami mai linzamin da 'yan gwagwarmayar neman sauyi na Houtsi a Yemen suka harba zuwa birnin Riyad na kasar Saudiyya, kirar Iran ne.
-
Antonio Guterres Ya Kira Yi Amurka Da Ta Girmama Yarjejeniyar Nukiliyar Iran
Dec 14, 2017 02:50Babban magatakardar Majalisar Dinkin Duniya ya kara da cewa yarjejeniyar ce kadai hanyar da za ta tabbatar da kasantuwar shirin na Iran na zaman lafiya ne.
-
Antonio Guterres Ya Ce Makami Mai Linzami Da Aka Harba Cikin Kasar Saudiyya Ba Kirar Iran Ba Ce
Dec 12, 2017 08:31Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa: Babu wani dalili ko hujja da za a dogara da ita kan cewa makami mai linzami da aka harba daga kasar Yamen zuwa filin jirgin saman Sarki Khalid na Saudiyya kirar kasar Iran ce.
-
Jumhuriyar Musulunci Ta Iran A Shirye Take Ta Tallafawa Kungiyayi Masu Gwagwarmaya A Palasdinu
Dec 12, 2017 02:59Babban kwamandan dakarun Qudus na dakarun kare juyin juya halin Musulunci a Iran (IRGC) ya bayyana cewa rundunarsa a shirye take ta tallafawa kungiyoyi masu gwagwarmaya da yahudawan Sahyoniya a Palasdinu.