Antonio Guterres Ya Kira Yi Amurka Da Ta Girmama Yarjejeniyar Nukiliyar Iran
Babban magatakardar Majalisar Dinkin Duniya ya kara da cewa yarjejeniyar ce kadai hanyar da za ta tabbatar da kasantuwar shirin na Iran na zaman lafiya ne.
Kamfanin dillancin labarun Associated Press da ya nakalto maganganun na babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya da safiyar yau alhamis ya kuma yi watsi da zargin shugaban kasar Amurkan na cewa Iran ba ta aiki da yarjejeniyar.
A wani gefen, babban magatakardar Majalisar Dinkin Duniyar ya jinjinawa kasashen turai da suka hada Faransa, Birtaniya, Jamus da kuma tarayyar turai da suka nuna cikakken goyon bayansu ga ci gaba da aiki dayarjejeniyar.
Har ila yau, Guterres ya gargadi shugaban na Amurka da kada ya sake yin wata baranbaramar da za ta haddasa matsala a cikin yankin gabas ta tsakiya