-
Shuwagabannin Kasashen Kwamitin CBLT, Sun Sha Alwashin Murkushe Boko Haram
Dec 16, 2018 16:35Shuwagabannin kasashe mambobin kwamitin tafkin Chadi, cewa da (CBLT), sun sha alwashin ganin bayan kungiyar Boko haram domin kawo karshen tsatsauran ra'ayi a yankin.
-
An Kai Harin Ta'addanci A Arewacin Kasar Kamaru
Dec 15, 2018 19:22Kamfanin dillancin labaran Associated Press ya ambato cewa; Wasu mata biyu ne su ka kai harin kunar bakin wake a garin Kolofata da yake kan iyaka da Najeriya, wanda ya yi sanadin jikkatar mace guda da kuma wata budurwa yar shekaru 12
-
Kamaru : Amurka Ta Bukaci Tattaunawa Tsakanin Gwamnati Da 'Yan Ware
Dec 14, 2018 03:59Gwamnatin Amurka ta bukaci gwamnati da masu fafatukar a ware na Kamaru dasu tattauna ba tare da wata-wata ba.
-
Kamaru : Kwace Gasar Cin Kofin Afrika, Rashin Adalci Ne
Dec 03, 2018 10:49Kasar kamaru ta bayyana kwace mata nauyin karbar bakuncin gasar cin kofin AFrika ta 2019 da rashin adalci.
-
Kamaru : An Kafa Kwamitin Karbar Makamai Daga 'Yan Boko Haram
Dec 02, 2018 15:35A Kamaru, an kafa wani kwamitin kasa da aka aza wa yaunin karbar makaman yaki a yankunan dake fama da rikici da suka hada da yankin arewa mai nisa da kuma na masu magana da turancin Ingilishi.
-
Hukumar CAF Ta Kwace Damar Daukan Bakuncin Gasar Cin Kofin Afirka Daga Kasar Kamaru
Dec 01, 2018 05:24Hukumar Kwallon Kafa ta Afirka (CAF) ta sanar da kwace damar daukar bakuncin gasar cin kofin kasashen Afirka (AFCON) na shekara ta 2019 da ta ba wa kasar Kamaru saboda alamu suna nuna cewa kasar ba ta shirya wa hakan ba.
-
Boko Haram : Kasashen Yankin Tafkin Chadi Sun Bukaci Taimakon Duniya
Nov 30, 2018 03:36Kasashen Najeriya da Nijar da Chadi da kuma Kamaru, sun bukaci taimakon kasashen duniya a yakin da suke da kungiyar Boko Haram.
-
Za'a Fara Yi Wa Wasu Shugabannin 'Yan Awaren Kamaru Da Ake Zargi Da Ayyukan Ta'addanci Shari'a
Nov 29, 2018 17:47An sanar da ranar da za a fara yi wa wasu shugabannin 'yan awaren kasar Kamaru su 10 da aka dawo da su kasar daga Nijeriya shari'a bisa zargin gudanar da ayyukan ta'addanci wadanda ana iya yanke musu hukuncin kisa idan har aka same su da laifi.
-
Wata 'Yar Kunar Bakin Wake Ta Raunana Mutane 29 A Kasar Kamaru
Nov 28, 2018 17:29Jami'an tsaron kasar Kamaru sun tabbatar da samun raunin mutane 29 sakamakon wani harin kunar bakin wake da wata mace ta kai a yau din nan Laraba a garin Amchide da ke yanki arewa mai nisa na kasar.
-
Kamaru : An Saki 'Yar Jarida Mimi Mefo
Nov 11, 2018 05:37Hukumomi a Jamhuriya Kamaru, sun sallami 'yar jaridar nan Mimi Mefo wadda aka cafke kwanaki biyu da suka gabata bisa zargin yada labarin karya.