Dec 03, 2018 10:49 UTC
  • Kamaru : Kwace Gasar Cin Kofin Afrika, Rashin Adalci Ne

Kasar kamaru ta bayyana kwace mata nauyin karbar bakuncin gasar cin kofin AFrika ta 2019 da rashin adalci.

Wannan dai shi ne karon farko da mahukuntan Kamarun sukayi bayyani tun bayan da hukumar kwallon kafa ta Afrika (CAF), ta sanar da kwace nauyin gudanar da gasar ta 2019 ga hannun Kamaru.

Da yake bayyani kan hakan kakakin gwamnatin kasar Issa bakary, ya bayyana matakin da rashin adalci ga kamfanonin na cikin gida da shugaban kasar da al'ummar kasar ta Kamaru, game da kokarin da suke na ganin cewa kasar ta karbi bakuncin gasar ta 2019.

Matakin hukumar ta CAF dai ya fusata 'yan kasar ta Kamaru da dama.

Tags