AFCON U20 : Mali Ta Lashe Kofin Afrika Na Matasa
Mali ta lashe kofin gasar cin kofin kwallon kafa na Afrika na 'yan kasa da shekaru ashirin, da aka kammala jiya Lahadi a filin wasa na Seyni Kunce, na birnin Yamai a Jamhuriya Nijar.
Mali ta samu nasarar ce, bayan fafatawa ta wasan karshe da Senegal, wanda ya kai ga bugun daga kai sai mai tsaron gida, bayan da suka shafe mintuna 120 da karin lokaci a canjaras.
A cikin mintina 16 ne, dan wasan Mali, Bubakar Traore ya zura kwallo a ragar Senegal, sai kuma a cikin minti na 75, Senegal ta rama kwallon da aka zura mata, inda suka tashi kunnen doki 1-1, aka kuma kai ga karon lokaci ba tare da zura kwallo ba.
A zagayen bugun daga kai sai mai tsaron gidan ne Mali ta samu nasara kan Senegal da kwallaye 3-2.
Mali wacce ta doki kofin, da Senegal wacce ta zo ta biyu a gasar da kuma Senegal wacce ke a matsayi na uku da kuma Najeriya wacce ta zo matsayi na hudu, su ne zasu wakilci nahiyar a gasar cin kofin duniya na na ‘yan kasa da shekaru 20 da kasar Poland za ta karbi bakunci daga ranar 23 ga watan Mayu zuwa 15 ga watan Yuni na wannan shekara.