An Yi Garkuwa Da Wani Tsohon Minista A Kamaru
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i35653-an_yi_garkuwa_da_wani_tsohon_minista_a_kamaru
Hukumomin jamhuriyar Kamaru sun ce, an yi garkuwa da wani tsohon minista a yankin masu magana da turancin Ingilishi dake shiyyar arewa maso yammacin kasar.
(last modified 2019-04-27T14:25:10+00:00 )
Mar 21, 2019 14:38 UTC
  • An Yi Garkuwa Da Wani Tsohon Minista A Kamaru

Hukumomin jamhuriyar Kamaru sun ce, an yi garkuwa da wani tsohon minista a yankin masu magana da turancin Ingilishi dake shiyyar arewa maso yammacin kasar.

Emmanuel Ngafeson, wanda ya taba rike mukamin sakatare a ma'aikatar shari'a ta kasar mai kula da sha'anin gidajen yari, an yi garkuwa da shi ne a Bamenda, birnin mafi girma a yankin dake fama da yaki tsakanin dakarun gwamnati da mayakan dake fafatukar a ware.

Duk da cewa babu wata kungiya data dau alhakin garkuwa da tsohon ministan, ammam gwamnatin aksar ta dora alhakin hakan ga mayakan 'yan a ware na kasar.

Gwamnatin kasar ta kuma ce tana daukar dukkan matakan da suka dace don tabbatar da an sako tsohon ministan.

Dama kafin hakan an yi garkuwa da wasu 'yan wasan kwallon kafa a ranar Laraba data gabata, a yankin na Buea.