Feb 18, 2019 04:36 UTC
  • An Sako Daliban Da Aka Sace A Kamaru

Rahotanni daga Jamhuriya Kamaru, na cewa an sako daliban makarantar nan kimanin 200 da aka sace ranar Asabar data gabata a birnin Bamenda dake arewa maso yammacin kasar.

Labarin dai ya fito ne daga cocin lardin Kumbo, dake a nisan kilomita tamanin daga birnin Bamenda dake yankin masu magana da turancin ingilishi.

Anndai sace daliban ne su 170 da suka hada da jami'an tsaro biyu da kuma wani malamin makaranta da 'ya'yansa biyu da sanyin safiyar ranar Asabar data gabata, a makarantar kwaleji ta Saint Augustin College dake lardin Kumbo.

Cocin ta Kumbo ta bata fayyace yadda aka sako daliban ba, amma ta bukaci iyayen daliban dasu zo su karbi yaransu, tare kuma da sanar da rufe makarantar.

Wasu majoyi daga yankin sun ce malaman cocin ne suka jagoranci tattaunawar neman sako daliban da akayi garkuwa dasu, bisa sharadin cewa za'a rufe makarantar.

Cocin ta bayyana cewa da sojoji sun shiga lamarin da anyi hasara rayuka.

Wanann dai shi ne karo na biyu mafi girma da ake fusknatr irin wannan lamari na sace dalibai a yankin, tun bayan barkewar rikicin a wannan yankin mai nasaba da masu fafatukar ballewa dake dauke da makamai da kuma jami'an tsaron kasar ta Kamaru.

Tags