Dec 16, 2018 16:35 UTC
  • Shuwagabannin Kasashen Kwamitin CBLT, Sun Sha Alwashin Murkushe Boko Haram

Shuwagabannin kasashe mambobin kwamitin tafkin Chadi, cewa da (CBLT), sun sha alwashin ganin bayan kungiyar Boko haram domin kawo karshen tsatsauran ra'ayi a yankin.

Bangarorin sun bayyana hakan ne a yayin taron gaggawa na shuwagabannin kasashe mambobin kwamitin na CBLT, da ya gudana a ranar Asabar a Abuja fadar gwamnatin Najeriya.

A sanarwar karshen taron da suka gudanar, shuwagabannin sun jaddada ci gaba da matakan da suka dauka na murkushe matsalar tsaro mai nasaba da Boko Haram a yankin tafkin na Chadi.

Taron ya kuma yaba wa kwamitin tsaro na kungiyar tarayyar Afrika (AU) kan sabunta wa'addin aikin rundinar hadin gwiwa ta kasashen yankin kan yaki da kungiyar ta Boko Haram na shekara mai zuwa ta 2019. 

Haka zalika shuwagabanin kasashen sun bayyana sahihiyar godiya ga abokan huldarsu da kuma kasashen duniya kan tallafin da suke basu akan yaki tsatsauran ra'ayi na kungiyar Boko Haram.

Taron da aka kawo karshensa a ranar Asabar, ya samu halartar shuwagabanin kasashen   Chadi, Nijar da Najeriya, da kuma shugaban gwamnatin Kamaru, tare da halartar wakilai na kasashen Benin da Jamhuriya Afrika ta Tsakiya.

Tags