Pars Today
Gwamnatin Jamhuriya Kamaru, ta ware kudade da yawansu ya kai Bilyan 12,7 na CFA, kwatancin Dalar Amurka, Miliyan 22,7, domin agaza wa jama'a a yankin masu magana da harshen Ingilishi dake fama da rikici a kasar.
Kamfanin dillancin labarun Xinhua na kasar sin ya ambato majiyar tsaron kasar Kamaru na cewa mutane 3 sun mutu ne sanadiyyar harin kunar bakin wake da aka kai a yankin Limani da ke arewacin kasar ta kamaru
Gwamnatin kasar Kamaru ta musanta rahoton da kungiyar kare hakkokin bil'adaman na ta Amnesty International ta fitar kan rikicin da ke faruwa a yankin masu magana da harshen Ingilishi na kasar tana mai bayyana rahoton a matsayin tsagoron karya kawai.
'Yan Boko Haram sun kai harin kunar bakin wake a kusa da wata makarantar gwamnati a yankin Limani na arewacin kasar Kamaru.
Majiyar labarai daga yankunan masu magana da harshen turancin Ingilishi a kasar Kamaru ta bayyana cewa an kashe soja guda a jiya Asabar a wani harin da yan tawaje a yankin suka kai sojojin a sansanoninsu.
Wasu 'yan bindiga sun kai hari tare da kashe mutum 6 a arewacin kasar Kamaru
Kungiyar kasa da kasa mai sanya ido kan tashe-tashen hankula a duniya ta International Crisis Group ta ce; Tashe-tashen hankula a kasar Kamaru suna ci gaba da lashe rayukan mutane.
Rahotanni daga kasar Kamaru na cewar akalla yan aware 34 aka kashe a garin Menka dake Yankin da ake amfani da Turancin Ingilishi
Wata kotu a kasar Kamaru ta yanke hukunci daurin shekaru 15 a gidan Kaso kan wasu shugabani na yankin dake amfani da turancin inglishi bisa laifin ta'addanci a kasar
A ci gaba da katsa landan din da kasar Amurka ke yi a harakokin cikin gidan kasashen Afirka, Jakadan Amurka a r Kamaru ya zargi hukumomin kasar da kisan masu son ballewa daga cikin kasar