Amurka Ta Zargi Kamaru Da Kisan Masu Son Ballewa Daga Kasar
A ci gaba da katsa landan din da kasar Amurka ke yi a harakokin cikin gidan kasashen Afirka, Jakadan Amurka a r Kamaru ya zargi hukumomin kasar da kisan masu son ballewa daga cikin kasar
Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya nakalto Peter Barlerin jakadan kasar Amurka a kamaru yana tuhumar dakarun gwamnatin kasar da kisan masu amfani da harshen turancin Ingilishi masu son ballewa daga kasar, inda ya bukaci a bawa yankunan dake son ballewa damar gudanar da zaben raba gardama domin tattance ra'ayinsu.
Peter Barlerin ya kara da cewa jami'an tsaron kasar ta Kamaru na aiwatar da kisa tare kame mutanan yankin ba tare da sammacin kotu ba, sannan kuma sun kone gidajen mutane a yankin tare da kwashe dukiyoyinsu a matsayin ganima.
Wannan bayani na Jakadan kasar Amurka a kamaru na zuwa kwana guda kacal bayan da ya gana da Shugaba Paul Biya a jiya alhamis.
Masu magana da harshen turancin Ingilishi a kasar Kamaru su ne kasahi 20% na yawan mutanen kasar ,da suka kai kimani miliyon 20 .
Kididdiga ta nuna cewa tun watan Octoban shekara ta 2017 da ya gabata, an kashe jami'an tsaro kasar ta Kamaru 28 a yankin.