An Sace Dalibai 200 A Kamaru
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i35254-an_sace_dalibai_200_a_kamaru
Rahotanni daga Kamaru na cewa wasu mayaka sun yi awan gaba da dalibai kimanin 200 a garin Bamenda dake yankin masu magana da turancin Ingilishi.
(last modified 2019-02-17T10:28:44+00:00 )
Feb 17, 2019 10:28 UTC
  • An Sace Dalibai 200 A Kamaru

Rahotanni daga Kamaru na cewa wasu mayaka sun yi awan gaba da dalibai kimanin 200 a garin Bamenda dake yankin masu magana da turancin Ingilishi.

Wata majiyar soji ta shaidawa masu aiko da rahotanni cewa, an sace daliban ne wajajen karfe biyar na safiyar jiya Asabar, a makarantar kwaleji ta Saint Augustin dake lardin Kumbo dake nisan kilomita 80 daga Bamanda.

Majiyoyi da dama sun tabbatar da cewa mayakan sunyi awan gaba da daliban, saidai kawo yanzu babu cikaken bayani daga bangaren mahukuntan kasar

Wanann dai shi ne karo na biyu mafi girma da irin hakan take faruwa a wannan yankin, tun bayan barkewar rikicin yankin mai nasaba da masu fafatukar balewa dake dauke da makamai da kuma jami'an tsaron kasar ta Kamaru.