An Kashe Mutum 6 A Arewacin Kamaru
Wasu 'yan bindiga sun kai hari tare da kashe mutum 6 a arewacin kasar Kamaru
Hukumomin kasar Kamaru sun sanar da cewa a jijjifin safiyar wannan juma'a, wasu 'yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun kai hari kauyen Mayo-Sava dake arewa mai nisa tare da kashe mutum 6.
Saidai mazauna yankin na zargin mayakan kungiyar Boko haram da kai harin.
Tun daga lokacin da mayakan boko haram suka fara kai hare-haren ta'addanci a arewacin kamaru a shekaru 2015, wannan yankin na Mayo-Sava ya fuskanci hare-haren boko haram da dama.
Tun a shekarar 2009 ne kungiyar boko haram ta fara kai hare-haren ta'addanci a arewacin Najeriya, sannan a shekarar 2015, ta fadada kai hare-harenta zuwa kasashen Nijer, Tchadi da kuma arewacin Kamaru.
Kididdigar MDD ta ce rikicin ya hallaka sama da mutane dubu 20 sannan kuma ya raba wasu dama da miliyan biyu da mahalinsu.