Pars Today
Motocin Buldoser sun rusa gidajen mutane a unguwar Kibera a wajen birnin Nairobi babban birnin kasar Kenya wanda ya bar dubban mutane babu wurin zama.
Kungiyoyin fararen hula a Kenya sun bukaci mahukuntan kasar da su dauki matakin bin kadin 'yan kasar ta Kenya da suke gudanar da ayyuka a kasar Saudiyya sakamakon bullar labarin yadda ake cin zarafinsu.
Kakakin 'yan sandan kasar Kenya Charles Oyino ne ya sanar da cewa an dasa bom din ne a bakin hanya a gabacin kasar wanda kuma ya yi sanadin mutuwar mutane bakwai
Ma'aikatar sifiri ta kasar Kenya ta basa sanarwan gano burbushin na karamin jirgin saman kasar da ya fadi a tsakiyar kasar a ranar Talatan da ta gabata ba.
A kasar kenya an dakakar da binciken da ake na neman karamin jirgin nan da ya bata, dauke da fasinjoji takwas da mambobi biyu a ranar Talata.
Wakilan al'ummar Kenya sun jaddada muhimmancin ci gaba da samun hadin kai da fahimtar juna a tsakanin mabiya addinan kasar.
Ministan harkokin wajen kasar Somalia ya musanta labaran da aka watsa na cewa kasarsa da kasar Kenya makobciya sun tattauna batun kan iyakokin kasashen biyu na kan cikin ruwa.
Bullar cutar kwalara a sansanin 'yan gudun hijira na Dadaab da ke kasar Kenya ta lashe rayukan mutane akalla bakwai ciki har da kananan yara.
Rahotanni daga Kenya sun bayyana cewar alal akalla mutane 21 sun rasa rayukansu sakamakon fashewar wata madatsar ruwa saboda ruwan sama da kamar da bakin kwarya da aka yi a daren jiya Laraba wayewar garin Alhamis.
Gwamnatin kasar Kenya ta gargadi wasu daga cikin kasashen larabawan yankin tekun Fasha musamman UAE dangane da ci gaba da dagula lamurra da suke yi a kasar Somalia.