Musulmi Da Kirista Sun Jaddada Hadin Kai A Tsakaninsu A Kasar Kenya
(last modified Mon, 28 May 2018 06:47:45 GMT )
May 28, 2018 06:47 UTC
  • Musulmi Da Kirista Sun Jaddada Hadin Kai A Tsakaninsu A Kasar Kenya

Wakilan al'ummar Kenya sun jaddada muhimmancin ci gaba da samun hadin kai da fahimtar juna a tsakanin mabiya addinan kasar.

A jawabinsa a wajen bikin bude wani katafafen Masallaci mafi girma na biyu a birnin Nairobi fadar mulkin kasar Kenya: Wakilin mabiya addinin kirista a Majalisar Dokokin kasar Timoso Vaniani ya bayyana cewa: Al'ummar Kenya da suka hada da musulmi da kirista dukkaninsu Allah guda suke bautawa, kamar yadda suka yi tarayya a kan akidu masu yawa, don haka yana da kyau a dauki wajajen bauta irin Masallatai da Majami'u a matsayin cibiyoyin karfafa samun hadin kai da taimakekkeniya a tsakanin mabiya addinai.

A nashi bangaren Najib Bilal ministan ma'aikatar yawon shakatawa da bude ido ta kasar Kenya ya jaddada wajabcin maida wajajen bauta irin Masallaci da Majami'a a matsayin cibiyoyin fadakarwa kan kyawawan dabi'u, ilimantarwa da cusa ruhin dan Adamtaka a tsakanin mabiya addinai.

Har ila yau Yusuf Enzibu shugaban Majalisar Kolin Harkokin addinin Musulunci a kasar ta Kenya ya jaddada muhimmancin hadin kai da fahimtar juna a tsakanin mabiya addinai da mazhabobi.