Feb 17, 2019 06:45 UTC
  • Kasar Kenya Ta Kirayi Jakadanta Daga Kasar Somaliya

A jiya Asabar ne kasar ta Kenya ta kirayi jakadanta Lucas Tumbo daga Magadishu bisa sabanin da ya kunno kai a tsakanin kasashen biyu akan iyakokin ruwa

Ministar harkokin wajen kasar Kenya, Monica Juma ce ta sanar da cewa; An kirayi jakadan ne saboda sabanin da kasashen biyu suke da shi akan iyakokin ruwa na kasashen biyu

Kenya tana zargin kasar Somaliya da kokarin gayyato kamfanonin man fetur domin hako man da kuma iskar gas a cikin iyakokin ruwan da kasashen biyu suke da sabani akai

Kasar Kenya tana cikin kawancen da yake fada da kungiyar al-shabab ta kasar Somaliya.

Tags