Kenya : An Dakatar Da Binciken Jirgin Saman Da Ya Bace
A kasar kenya an dakakar da binciken da ake na neman karamin jirgin nan da ya bata, dauke da fasinjoji takwas da mambobi biyu a ranar Talata.
A jiya Laraba Kenya ta dakatar da neman karamin jirgin a karo na biyu sakamakon rashin kyawun yanayi.
Kwamishina mai kula da yankin Nyandarua, Boaz Cherutich, ya ce tawagar masu binciken jirgin suna fuskantar kalubalen rashin kyawun yanayi a dajin Aberdares, inda daga wajen ne aka daina jin duriyar jirgin.
Karamin jirgin saman, samfurin Fly-SAX, yana dauke ne da fasinjoji 8 da ma'aikatan jirgin guda 2, kamar yadda kamfanin jirgin ya bayyana cikin wata sanarwa a daren Talata.
Hanyoyin sadarwa da jirgin sun katse ne da yammacin ranar Talata a yayin da jirgin ke kan hanyarsa daga garin Kitale na arewa maso yammacin Kenya zuwa birnin Nairobi.