Pars Today
Jami'an tsaron kasar Somalia sun sami nasarar tsarkake wani yanki na kan iyaka da kasar Kenya daga samuwar yan ta'adda ta kungiyar al-shabab.
Rundunar 'yan sandan Kenya ta sanar da cewa: Wani bom ya tashi a kan hanyar shigewar tawagar 'yan sandan kasar a yankin Mararani da ke gabashin kasar Kenya kusa da kan iyaka da kasar Somaliya.
Sojojin gwamnatin kasar Somaliya sun ce sun kwato garin Balad Hawo da ke kan iyakan kasar da kasar Kenya daga hannun 'yan kungiyar ta'addancin nan ta Al-Shabab bayan kame garin da suka yi a safiyar yau Litinin.
Shugaban Kasar Kenya ya zargi 'yan adawar kasar da kokarin wurga kasar Kenya cikin rikici da rudani ta hanyar amfani da kotun kolin kasar da ta soke zaben shugabancin kasar da aka gudanar cikin yanci da tsabta.
Hukumar zabe mai zaman kanta na kasar Kenya (IEBC) ta ce tana kan bakarta na sake gudanar da zaben shugaban kasar da aka soke a kwanakin baya duk kuwa da adawa da kuma damuwar da babbar jam'iyyar hadaka ta 'yan adawan kasar NASA take nunawa.
Gamayyar jam'iyyun siyasa ta yan adawa a kasar Kenya wacce ake kira NASA a takaice ta bukaci magoya bayan gamayyar su tallafa da kudade don fara yakin neman zaben shugaban kasa wanda za'a gudanar a cikin watan Octoba mai zuwa.
Hukumar zabe ta kasa a Kenya ta nada wasu sabbabin manyan jami'ai shida don tsara sabon zaben shugaban kasar.
Mayakan kungiyar Al- shabab sun kai wasu tagwayen hare-hare a wasu kauyukan yankin Lamu County na kasar Kenya tare da yiwa mutane 4 na cikin kauyen yankan rago
madugun 'yan hamayyar siyasar Kasar Kenyar, Raila Odinga ya ce ba a shirye suke ba da a kafa gwamnatin hadaka da su.
Hukumar Zabe a kasar Kenya ta bayyana ranar 17 ga wata Oktoba mai zuwa a matsayin ranar da za'a sake zaben shugaban kasa tsakanin shugaban mai ci Uhuru Kenyata da kuma Raila Odingi shugaban babbar jam'iyyar yan adawar kasar.