Mayakan Al-shabab Sun Yiwa Mutane 4 Yankan Rago A Kenya.
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i23799-mayakan_al_shabab_sun_yiwa_mutane_4_yankan_rago_a_kenya.
Mayakan kungiyar Al- shabab sun kai wasu tagwayen hare-hare a wasu kauyukan yankin Lamu County na kasar Kenya tare da yiwa mutane 4 na cikin kauyen yankan rago
(last modified 2018-08-22T11:30:39+00:00 )
Sep 07, 2017 06:36 UTC
  • Mayakan Al-shabab Sun Yiwa Mutane 4 Yankan Rago A Kenya.

Mayakan kungiyar Al- shabab sun kai wasu tagwayen hare-hare a wasu kauyukan yankin Lamu County na kasar Kenya tare da yiwa mutane 4 na cikin kauyen yankan rago

Kamfanin dillancin labaran Reuteus daga Mumbasa ya nakalto Gilbert Kitty daya daga cikin magabatan tsaron yankin Lamu County na kudu maso gabashin kenya a jiya laraba na cewa mayakan kungiyar ta'addancin nan ta As shabab ta kai wani hari a kauyukan Silisni-Mashambani da Bobo na kudu maso gabashin kasar.

A watan Augustan da ya gabata ma, mayakan kungiyar Al- shabab din sun yiwa mutane 4 yankan rago a wani hari da suka kai kauyukan na yankin, a watan yulin da ya gabata ma mayakan na As shabab sun hallaka mutane 9 a yankin.

Tun bayan da kasar kenya ta aike da dakarunta zuwa kasar Somaliya domin yaki da kungiyar Al- shabab, arewa da wasu yankunan gabashin kasar ta kenya ke fuskanta hare-haren ta'addanci daga mayakan kungiyar Al- shabab.