Pars Today
Wasu 'yan bindiga sun kai hari kan wata coci tare da hallaka jami'an 'yan sanda biyu dake tsaron cocin a kudancin kasar Kenya.
Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta da mataimakinsa William Ruto sun ja kunnen babban alkalin kotun kolin kasar dangane da soke zaben shugaban kasar da yayi da cewa a nan gaba su ma za su yi na su abin da ya dace din.
'Yan adawa a kasar Kenya ta yi maraba da matakin kotun kolin kasar na soke zaben shugaban kasar da aka gudanar a watan jiya.
Kotun kolin kasar Kenya ta sanar da soke zaben shugaban kasar da aka gudanar a kasar, bisa hujjar cewa an tafka magudi.
Hare-Haren yan ta'adda a daren ranar Talatan da ta gabata ya yi sanadiyyar raunata mutum gusa, sannan yan ta'addan sun arce zuwa kan iyakokin kasashen biyu.
Kungiyar kare hakkin bil'adama ta "Human Right Watch" ta ce; 'yan sandan kasar Kenya sun yi amfani da karfi akan 'yan hamayyar siyasa a lokacin da ake zabe da kuma bayansa.
Kungiyar kare hakkin bil-adama ta Human Rights Watch, ta zargi 'yan sandan kasar Kenya ta take hakkin jama'a bayan sanar da sakamakon zaben kasar da aka yi a farkon wannan wata na Agusta.
'Yan Adawa a kasar Kenya sun bukaci gwamnati da ta soke zaben shugaban kasa.
'Yan adawan kasar Kenya sun shigar da kara kotun koli ta kasar suna masu watsi da sakamakon zaben shugaban kasar da aka sanar na cewa shugaban kasar mai ci Uhuru Kenyatta shi ne ya lashe zaben.
An bude tashar talabijin ta farko mallakin musulmi a kasar Kenya wadda za ta rika gabatar da shirye-shirye na addinin muslunci.