Kotu Ta Soke Zaben Shugaban Kasa Da Aka Gudanar A Kasar Kenya
(last modified Fri, 01 Sep 2017 11:19:59 GMT )
Sep 01, 2017 11:19 UTC
  • Kotu Ta Soke Zaben Shugaban Kasa Da Aka Gudanar A Kasar Kenya

Kotun kolin kasar Kenya ta sanar da soke zaben shugaban kasar da aka gudanar a kasar, bisa hujjar cewa an tafka magudi.

Kamfanin dillancin labaran AFP daga birnin nairobi ya bayar da rahoton cewa, babban alkalin kotun kolin kasar Kenya David Maraga shi ne ya sanar da hakan, inda ya ce an gudanar da wasu abubuwan da suka sabawa kundin tsarin mulkin kasar a lokacin zaben, saboda kotu ta soke shi.

Ya kara da cewa a halin yanzu Uruhu Kenyatta ba shugaban kasar Kenya ba ne, kuma kotu ta bayar da umarnin da a shirya wani zaben daga zuwa kwanaki sittin.

Madugun adawa na kasar Reila Odiga ya bayyana farinciki maras misiltuwa da jin hakan, kamar yadda magoya bayan jam'iyyun adawa a fadin kasar suke ta murna a kan hakan.