Kungiyar kare hakkin Bil-adama ta zargi Kenya
(last modified Mon, 28 Aug 2017 19:01:36 GMT )
Aug 28, 2017 19:01 UTC
  • Kungiyar kare hakkin Bil-adama  ta zargi Kenya

Kungiyar kare hakkin bil-adama ta Human Rights Watch, ta zargi 'yan sandan kasar Kenya ta take hakkin jama'a bayan sanar da sakamakon zaben kasar da aka yi a farkon wannan wata na Agusta.

Kungiyar kare hakkin bil-adama  ta Human Rights Watch, ta zargi 'yan sandan kasar Kenya ta take hakkin jama'a bayan sanar da sakamakon zaben kasar da aka yi na ranar 8 ga wannan watan na Agusta da muke ciki.

Rahotanni sun bayyana cewa akalla mutane 12 ne aka ne suka rasa rayukansu a yayin hargitsin bayan zaben, ciki kuwa har da wani jariri dan wata shida da haihuwa.

ko baya ga hakan akwai ma wasu sama da mutum 100 da suka ji jikkata sakamakon dukan da aka ce jami'an 'yan sanda suka yi masu.

Masu adawa da nasarar shugaba Uhuru Kenyatta na kasar, sun tayar da bore ne jim kadan bayan bayyana rashin gamsuwa da sakamakon zaben da jagoran 'yan adawa Raila Odinga  ya yi, inda suka yi ta tayar da jijiyoyin wuya a Nairobi da ma wasu manyan birane na kasar.