-
Jagora: Iran Ba Ta Shirin Fara Yaki Da Wata Kasa, Amma Za Ta Kare Kanta
Nov 28, 2018 17:29Jagoran juyin juya halin Musulunci, Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewar Iran ba ta neman fara yaki da duk wata kasa, to amma wajibi ne sojojin Iran su kara irin karfin da suke da shi don jan kunnen duk wani mai shirin wuce gona da iri kan kasar ta Iran.
-
Iran : Jagora Ya Jinjinawa Hukumar Tsaron Farin Kaya
Oct 28, 2018 19:25Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya jaddada bukatar ganin ayyukan hukumar tsaron farar kaya ta kasar ya hada dukkanin bangarori da nufin rusa makirce-makircen makiya kan kasar Iran.
-
Jagora Yayi Kakkausar Suka Ga 'Munafuncin' Kasashen Yammaci Kan Makaman Nukiliya
Sep 27, 2018 05:48Jagoran juyin juya halin Musulunci, Ayatullah Sayyid Ali Khamenei yayi kakkausar suka munafunci da siyasar harshen damon da kasashen yammaci suke yi dangane da batun amfani da makaman nukiliya, yana mai tunatar da su irin goyon bayan da suka ba wa tsohon shugaban kasar Iraki, Saddam Husseini a yayin da ya kallafa wa Iran a shekarun 1980.
-
Jagora: Manufar Takunkumin Da Bakar Farfagandar Makiya A Kan Iran, Ita Ce Kashe Gwiwar Al'umma
Sep 06, 2018 16:38Jagoran juyin juya halin Musulunci, Ayatullah Sayyid Ali Khamenei, ya bayyana cewar makiyan al'ummar Iran sun kakabawa Iran takunkumi da kuma ci gaba da yada bakar farfaganda a kanta ne saboda kashe gwiwan al'ummar kasar da kuma sanya musu yanke kauna cikin zukatansu.
-
Ayatollah Khamenei: Palastinawa Ne Kawai Za Su Ayyana Makomar Palastinu
Jun 11, 2018 17:01Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana makomar Palastinu yana hannun Palastinawa ne, kuma su ne kawai za su ayyana makomar na ta.
-
Jagora Ya Ja Kunnen Makiya Kan Kawo Wa Iran Hari, Ya Ba Da Umurnin Sake Dawo Da Aikin Nukiliya
Jun 04, 2018 18:20Jagoran juyin juya halin Musulunci, Ayatullah Sayyid Ali Khamenei, ya bayyana cewar matukar dai gigi ya debi makiya suka kawo wa Iran hari to kuwa za su debi kashinsu a hannu, yana mai ba da umurnin dawo da shirin tace sinadarin nukiliya da Iran ta dakatar daga gobe
-
Jagora: Ficewar Amurka Daga Yarjejeniyar Nukiliya Bai Zo Mana A Matsayin Ba Za Ta Ba
May 09, 2018 10:43Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewar sanarwar ficewa daga yarjejeniyar nukiliya da shugaban Amurka yayi a daren jiya bai zo masa a matsayin wani abin mamaki ba, yana mai cewa al'ummar Iran za su ci gaba da riko da tafarkin da suke kai ba tare da tsoron wani ba.
-
Jagora: Al'ummar Iran Sun Kunyata Amurka, Birtaniyya Da 'Yan Amshin Shatansu
Jan 09, 2018 11:22Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewar cewa al'ummar Iran sun kunyata Amurka, Birtaniyya da sauran 'yan amshin shatansu yayin da suka fito don nuna goyon bayansu ga tsarin Musulunci da kuma yin Allah wadai da masu tada fitina.
-
Jagora: Makiya Suna Amfani Da Kudi Da Makamai Da 'Yan Korensu Wajen Haifar Da Rikici A Iran
Jan 02, 2018 17:10Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewar makiya al'ummar Iran suna amfani da hanyoyi mabambanta wajen cutar da al'umma da kuma tsarin Musulunci ta kasar.
-
Jagora: Tabbas Za A 'Yantar Da Palastinu Sannan Batun Mai Da Qudus Helkwatar Isra'ila Wata Gazawa Ce
Dec 06, 2017 11:13Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewar kokarin da Amurka ta ke yi na mayar da birnin Qudus a matsayin helkwatar haramtacciyar kasar Isra'ila wata gazawa ce daga bangarensu don kuwa matsalar Palastinu wani lamari ne da ya fi karfinsu, yana mai jaddada cewar ko shakka babu za a 'yanto kasar Palastinu daga mamayar sahyoniyawa.