-
Jagora Yayi Afuwa Wa Fursunoni Saboda Zagayowar Maulidin Annabi (s)
Dec 05, 2017 11:02Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei yayi afuwa ga wasu fursunoni da kuma rage wa'adin zaman gidan yari ga wasu don tunawa da murnar zagayowar Maulidin Manzon Allah (s).
-
Iran A Shirye Take Ta Yi Fada da Duk Wani Kokari Na Sake Kirkiro Wata Kungiyar Ta'addanci
Nov 24, 2017 05:16Babban hafsan hafsoshin sojojin Iran Manjo Janar Muhammad Baqeri ya bayyana jinjinawa nasarar da aka samu a kan kungiyar ta'addancin nan ta Daesh (ISIS) a kasashen Iraki da Siriya yana mai cewa dakarun kasar Iran a shirye suke su yi fada da duk wani kokari na makiya na kirkiro wata kungiya ta ta'addanci irin Da'esh din.
-
Jagora: Iran Ta Kawo Karshen Makircin Kirkiro Kungiyar Daesh Da Amurka Da Sahyoniyawa Suka Yi
Nov 22, 2017 18:20Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewar Iran ta samu nasarar ruguza makircin da Amurka da haramtacciyar kasar Isra'ila da wasu kasashen larabawan yankin Gabas ta tsakiya suka kitsa na kirkiro kungiyar ta'addancin nan ta Da'esh (ISIS).
-
Ayatullah Khamenei Ya Gana Da Shugaban Kasar Rasha Vladimir Putin
Nov 01, 2017 18:18Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewar irin nasarorin da ake samu a kasar Siriya a fadar da ake yi da ta'addanci na nuni da cewa Iran da kasar Rasha za su iya aiki tare wajen cimma manufofin da suka yi tarayya kanta yana mai cewa ko shakka babu ana iya mai da Amurka ta zamanto saniyar ware sannan kuma takunkumin da ta sanya wa kasashe su zamanto aikin baban giwa.
-
Ayat. Khamenei: Iran Ba Za Ta Taba Tattaunawa Kan Karfinta Na Soji
Oct 26, 2017 05:48Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewar Iran ba za ta taba tattaunawa da wani kan karfin da take da shi na kare kanta daga makiya ba, yana mai sake jaddada aniyar kasar Iran na ci gaba da kara irin karfin kariya da take da shi duk kuwa da maganganun da makiya suke yi.
-
Jagora Imam Khamenei Ya Aike Da Taimakon Makudan Kudade Ga Musulmin Rohingya
Oct 18, 2017 05:49Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya ware makudan kudaden da suka kai dala dubu 250 don taimakawa 'yan gudun hijiran musulman Rohingya na kasar Myammar don rage musu irin wahalhalun da suke ciki sakamakon ci gaba da kisan kiyashin da ake musu a kasar.
-
Jagora: Iran Za Ta Mayar Da Martani Ga Duk Wani Karen Tsaye Ga Yarjejeniyar Nukiliya
Sep 17, 2017 16:54Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya ja kunne da cewa Iran za ta ci gaba da girmama yarjejeniyar nukiliya da ta cimma da kasashen kungiyar 5+1, to sai dai za ta mayar da martani ga duk wani karen tsaye ga yarjejeniyar.
-
Shugaban Siriya Ya Gode Wa Jagora Da Al'ummar Iran Saboda Goyon Bayansu
Sep 15, 2017 05:49Shugaban kasar Siriya Bashar al-Asad ya bayyana godiyarsa ga Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei da sauran al'ummar Iran saboda irin goyon bayan da suke ba wa gwamnatinsa a fadar da take yi da ta'addanci.
-
Jagora: Iran Ba Za Ta Taba Mika Wuya Ga Mulkin Kama-Karyar Ma'abota Girman Kai Ba
Aug 03, 2017 10:57Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewar Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba ta taba kuma ba za ta taba mika kai ga mulkin kama-karya na ma'abota girman kai, yana mai cewa a halin yanzu Iran tana tsaya da kafafunta kyam sama da shekarun baya.
-
Ayat. Khamenei: Koda Wasa Harin Ta'addancin Tehran Ba Zai Kashe Gwuiwan Al'ummar Iran Ba
Jun 08, 2017 05:20Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewar koda wasa harin ta'addancin da aka kai birnin Tehran ba zai raunana gwiwan al'ummar Iran wajen fuskantar duk wata barazana ba, yana mai jaddada cewar da yardar Allah za a tumbuke tushen ta'addanci.