Ayat. Khamenei: Iran Ba Za Ta Taba Tattaunawa Kan Karfinta Na Soji
Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewar Iran ba za ta taba tattaunawa da wani kan karfin da take da shi na kare kanta daga makiya ba, yana mai sake jaddada aniyar kasar Iran na ci gaba da kara irin karfin kariya da take da shi duk kuwa da maganganun da makiya suke yi.
Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi wajen bikin yaye daliban jami'ar jami'an soji ta Imam Ali (a.s) da aka gudanar inda ya ce: Na sha fadi kuma yanzu ma zan fadi cewa karfin kariya da muke da shi ba abu ne da za mu tattauna kansa ko kuma neman yin sulhu ba.
Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: A yayin da ake magana kan batun kara karfin da ake da shi na kare kasarmu, to kuwa babu wani sassauci ko tattaunawa da yin sulhu da makiya. Don haka za mu ci gaba da karfafa irin karfin da muke da shi sama da yadda yake a da.
A wani bangare na jawabin nasa, Ayatullah Khamenei ya yi karin haske dangane da fushi da kuma damuwar da ma'abota girman kan duniya suke ciki sakamakon irin tasirin da Iran take da shi a yankin Gabas ta tsakiya inda yace hakan ne ya sanya makiyan yin dukkanin abin da za su iya wajen ganin sun raunana Iran, wanda ya ce cikin yardar Allah ba za su yi nasara ba.
A yayin bikin dai Jagoran ya mika lambobin yabo ga kwamandoji da kuma daliban jami'ar wadanda suka yi rawar gani tsawon shekara, kamar yadda kuma daliban jami'an suka gudanar da wani faretin ban girma don tabbatar da shirin da suke da shi na kare kasarsu daga duk wata barazana ta makiya.