-
Jagora: Juyin Juya Halin Musulunci Ya Samar Wa Al'ummar Iran Mutumci Da Kuma 'Yancin Kai
Jun 04, 2017 18:03Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewar juyin juya halin Musulunci da marigayi Imam Khumaini (r.a) ya jagoranta a Iran ya samar wa mutanen Iran mutumci da kuma 'yancin kai, yana mai sake jaddada aniyar al'ummar Iran na ci gaba da riko da tafarkin marigayi Imam.
-
Jagora Yayi Afuwa Wa Fursunoni 593 Don Murnar Zagayowar Ranar Aiko Manzo (s)
Apr 24, 2017 17:12Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei yayi afuwa ga wasu fursunoni da kuma rage wa wasu hukuncin da aka yanke musu na zaman gidan yari don murnar zagayowar ranar da aka aiko Ma'aikin Allah (s) a matsayin Annabi kuma Manzo ga dukkanin talikai.
-
Jagora: Makiya Na Kokarin Dagula Zaben Shugaban Kasar Iran
Apr 19, 2017 11:15Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya ja hankulan al'ummar Iran dangane da kokarin da makiyan kasar Iran suke yi wajen dagula zaben shugaban kasa da za a gudanar nan gaba yana mai kiransu da su fito kwansu da kwarkwatarsu don kunyata makiyan.
-
Sakon Jagora Na Ta'aziyyar Rasuwar Ayatullah Hashimi Rafsanjani.
Jan 09, 2017 06:22Ofishin jagoran juyin juya halin Musulunci ya fitar da sakon jagoran akan rasuwar Ayatullah Hashimi Rafsanjani.
-
Jagora: Rashin Kiyaye Dokokin Ubangiji Ita Ce Babbar Matsalar Kasashen Yammaci
Jan 02, 2017 17:52Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewar rashin kula da kuma girmama koyarwa ta addini da umurnin Ubangiji, su ne ummul aba'isin din matsalolin da kasashen Yammacin suke fuskanta duk kuwa da irin ci gaban ilimi da suke da su.
-
Ayatullah Khamenei Yayi Afuwa Wa Wasu Fursunoni Saboda Zagayowar Maulidi
Dec 16, 2016 17:11Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya amince da yin afuwa da kuma rage wa'adin zaman gidan yarin sama da fursunoni 1,200 don murnar zagayowar ranar Maulidin Manzon Allah (s).
-
Jagora: Amurka Ba Da Gaske Take Yi Wajen Kawar Da 'Yan ISIS Ba
Dec 11, 2016 11:18Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewar Amurka ba da gaske take yi ba a ikirarin da take yi na kawo karshen ta'addancin kungiyoyi masu kafirta musulmi, face dai kokari ma take yi wajen kiyaye wasu kungiyoyin 'yan ta'adda a yankin nan don cimma manufofinsu.
-
Jagora Imam Khamenei: Sakamakon Zaben Amurka, Ba Shi Da Wani Bambanci A Wajenmu
Nov 16, 2016 11:20Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewar Iran dai ba ta cikin wata damuwa dangane da sakamakon zaben kasar Amurka, to sai dai tana cikin shirin fuskantar koma mai zai faru, yana mai cewa sakamakon zaben ba shi da wani bambanci a wajen Iran.
-
Jagora: Sasantawa Da Amurka Ba Zai Magance Matsalolin Da Ake Fuskanta Ba
Nov 02, 2016 15:20Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewar shiryawa da Amurka ba zai taba magance matsalolin da kasar Iran take fuskanta ba, don kuwa Amurkan ba ta yi watsi da kiyayyar da take nunawa al'ummar Iran ba.
-
Jagora: Babban Kuskure Ne Tunanin Cewa Ba Za'a Iya Yin Nasara A Kan Amurka Ba
Oct 23, 2016 06:24Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewar babban kuskure ne tunanin cewa ba za a iya samun nasara a kan Amurka ba yana mai ishara da irin shan kashin da siyasar Amurka take ci gaba da yi a yankin Yammacin Asiya.