Jagora: Makiya Na Kokarin Dagula Zaben Shugaban Kasar Iran
(last modified Wed, 19 Apr 2017 11:15:21 GMT )
Apr 19, 2017 11:15 UTC
  • Jagora: Makiya Na Kokarin Dagula Zaben Shugaban Kasar Iran

Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya ja hankulan al'ummar Iran dangane da kokarin da makiyan kasar Iran suke yi wajen dagula zaben shugaban kasa da za a gudanar nan gaba yana mai kiransu da su fito kwansu da kwarkwatarsu don kunyata makiyan.

Ayatullah Khamenei ya bayyana hakan ne a wata ganawa da yayi yau din nan da manyan kwamandojin sojin kasa na Iran da sauran jami'an sojin inda ya ce makiya suna ji gaba da maganganun tunzurawa da nufin dagula zaben. Don haka ya zama wajibi mutane su ci gaba da yin taka tsantsan wajen ganin an gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya kara da cewa tsayin daka shi ne babban mabudin rusa dukkanin makirce-makircen makiya a kan al'ummar Iran tsawon shekarun da suka gabata. Don haka sai ya ce Ba Amurka ba ko da ma wani karfin da ke gabanta ne ba zai iya fada da duk wani tsari da ke da goyon bayan al'umma, suna sonsa shi ma yana kaunarsu ba.

A ranar 19 ga watan Mayun mai kamawa ne dai za a gudanar da zaben shugaban kasar na Iran karo na 12, inda a halin yanzu ake ci gaba da tantance 'yan takaran da suka yi rajistan sunayensu.