Ayatullah Khamenei Yayi Afuwa Wa Wasu Fursunoni Saboda Zagayowar Maulidi
Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya amince da yin afuwa da kuma rage wa'adin zaman gidan yarin sama da fursunoni 1,200 don murnar zagayowar ranar Maulidin Manzon Allah (s).
A cikin wata sanarwa da ya fitar a yau din nan Juma'a, Jagoran ya sanar da amincewarsa da bukatar da shugaban Ma'aikatar shari'a kuma Alkalin alkalan kasar Iran Ayatullah Sadeq Amoli Larijani ya gabatar masa na yin afuwa ga wasu fursunoni da ake tsare da su.
Rahotanni sun ce a kwanakin baya ne Ayatullah Amoli Larijani ya mika jerin sunayen wasu fursunoni kimanin 1231 da aka yanke musu hukunci a kotuna daban-daban na kasar Iran bisa wasu laifuffuka, inda ya bukaci amincewar Jagoran wajen yin musu afuwa gaba daya ko kuma rage musu wa'adin zaman gidan yarin da aka yanke musu.
A gobe Asabar 17 ga watan Rabiul Awwal ne za a gudanar da bukukuwan Maulidin Manzon Allah (s) da jikansa Imam Sadiq (a.s) limamin Shi'a na shida a duk fadin Iran da sauran kasashen duniya inda mabiya tafarkin Ahlulbaiti (a.s) suke.