Jagora: Rashin Kiyaye Dokokin Ubangiji Ita Ce Babbar Matsalar Kasashen Yammaci
Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewar rashin kula da kuma girmama koyarwa ta addini da umurnin Ubangiji, su ne ummul aba'isin din matsalolin da kasashen Yammacin suke fuskanta duk kuwa da irin ci gaban ilimi da suke da su.
Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana hakan ne a wata ganawa da yayi a safiyar yau Litinin da daliban jami'ar fasaha ta Sharif da ke birnin Tehran inda yayin da yake magana kan muhimmancin riko da koyarwar addini a daidai lokacin da ke neman ilimi ya bayyana cewar ci gaba ilimi a kan kashin kansa ba zai iya kawo kwanciyar ga kasa da wata al'umma ba tare da riko da koyarwa ta Ubangiji ba.
Ayatullah Khamenei yayi ishara da irin matsalolin na iyalai, yawaitar rikice da kashe-kashe, kisan kai da suka yi yawa da sauran muggan dabi'u da suke faruwa a tsakanin al'ummomin kasashen yammacin musamman a Amurka a matsayin sakamako na rashin riko da koyarwa ta addini da kasashen yammacin suke fuskanta.
Don haka sai Jagoran ya kirayi daliban da su ba da himma wajen riko da koyarwa ta addini da na juyin juya halin Musulunci a daidai lokacin da suke karatun na su a matsayin hanya guda da za ta iya tabbatar da ci gaba da hakika ga kasar Iran.