Ayatullah Khamenei Ya Gana Da Shugaban Kasar Rasha Vladimir Putin
Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewar irin nasarorin da ake samu a kasar Siriya a fadar da ake yi da ta'addanci na nuni da cewa Iran da kasar Rasha za su iya aiki tare wajen cimma manufofin da suka yi tarayya kanta yana mai cewa ko shakka babu ana iya mai da Amurka ta zamanto saniyar ware sannan kuma takunkumin da ta sanya wa kasashe su zamanto aikin baban giwa.
Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana hakan ne a wata ganawa da yayi da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin wanda ya iso nan Tehran a yau din nan don fara wata ziyarar aiki, inda yayin da yake ishara da irin matsayar da Iran da Rasha suka dauka wajen fada da ta'addanci a kasar Siriya da kuma irin nasarorin da ake samu ya bayyana cewar tsayin dakan da kasashen biyu suka yi a wannan agen na ci gaba da haifar da nasarori.
Haka nan kuma yayin da yake ishara da irin tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasashen duniya da Amurka take yi Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana cewar kasashen duniya ta hanyar hadin kai da aiki tare a tsakaninsu suna iya mai da Amurka saniyar ware da sanya makamin takunkumin da take gadara da shi ya zamanto ba shi da wani tasiri.
Shi a nasa bangaren shugaban kasar Rashan Vladimir Putin ya bayyana farin cikinsa da sake samun damar ziyartar Iran da kuma ganawa da Jagoran juyin juya halin Musuluncin inda ya bayyana muhimmancin da ke cikin kara karfafa alakar da ke tsakanin kasashen Iran da Rasha.
A yau ne shugaban kasar Rashan ya iso nan Tehran don halartar taron bangarori uku da ya hada shi da shugaban kasar Iran da na Azarbaijan Ilham Aliyev.