Ayatollah Khamenei: Palastinawa Ne Kawai Za Su Ayyana Makomar Palastinu
Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana makomar Palastinu yana hannun Palastinawa ne, kuma su ne kawai za su ayyana makomar na ta.
Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana hakan ne a wata ganawar shan ruwa da yayi da wasu gungun malaman jami'a da sauran manyan makarantu na Iran inda ya ce: A halin yanzu dai tsarin dimokradiyya wani tsari da aka yarda da shi a duniya. Don haka ne muka ce al'ummar Palastinu da suka hada musulmi da kiristoci da yahudawansu wadanda su ne 'yan asalin kasar su ne ya kamata a bar musu ragamar ayyana makomarsu.
Jagoran ya ce kamata a yi a gudanar da kuri'ar jin ra'ayin al'ummar Palastinu wadanda suke wajen tun kimanin shekaru 100 da suka gabata kai ko ma da shekaru 80 ne, duk abin da suka zaba sai a aiwatar da shi. Jagoran ya ci gaba da cewa wannan ita ce kawai hanya ta adalci ta magance matsalar Palastinu.
A wani bangare na jawabin na sa, Ayatullah Khamenei ya sake jaddada goyon bayan Iran da al'ummarta ga al'ummar Palastinu a kokarin da suke yi na 'yanto kasarsu daga hannun 'yan mamaya.